Wasiyyar Imam Ali (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na daya daga cikin manya-manyan nassosin Musulunci wadanda suka kunshi darussa na dabi'a, zamantakewa da siyasa, kuma haske ne mai shiryarwa ba ga 'ya'yansa da sahabbansa kawai ba, har ma ga dukkan mutane masu neman gaskiya da adalci.
Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) – ABNA — ya kawo maku cewa: Wasiyyar Imam Ali (AS) na daya daga cikin muhimman nassosin Musulunci da suka kunshi darussa na dabi’a da zamantakewa da siyasa, kuma haske ne mai shiryarwa ba ga ‘ya’yansa da sahabbansa kadai ba, har ma ga dukkan mutane masu neman gaskiya da adalci.
A cikin wannan wasiyyar Imam yana jaddada batu akan takawa a cikin murya mai ɗauke da soyayya da gargadi yana mai cewa: "Ku yi takawa, domin ita ce mafi alherin guzuri ga tafiya zuwa ga Allah". Imam As suna ɗaukan duniya a matsayin mai karewa kuma suna kira ga mutane da su yi guzuri domin rayuwa ta har bada madauwamiya.
A cikin wannan wasiyyar, adalci yana haskakawa kamar rana mai haske. Imam Ali (AS) yana cewa: “Ku yi wa makiyanku adalci, domin adalci shi ne ginshikin da kasa da sammai suke bisansa”. Imam Ali As Suna daukar adalci a matsayin muhimmin abu a kowane fanni na rayuwa. Ita Sallah tana da matsayi babba a cikin fadinsa: "Ku kiyaye sallah, domin ita ce ginshikin addini kuma tana tafiyar da rai zuwa ga mi'iraji".
Imam Ali (AS) yana daukar hakkin mutane musamman marayu da matalauta a matsayin amana na Ubangiji, yana mai cewa: “Ku kare hakkinsu”. Ya kuma jaddada kyawawan halaye: "Ku kyautata wa mutane kuma ku guji tsaurarawa". Haka nan kuma suna kira ga al'ummar musulmi da su hada kansu su dauki rarrabuwar kawuna a matsayin halaka.
Imam Ali (AS) yana ganin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna a matsayin nauyi da ke kan kowane musulmi, daga karshe ya gabatar da hakuri a matsayin mabudin tsira: “Ku yi hakuri a cikin cutarwa". Wannan wasiyyar jagora ce ta har abada ga rayuwar mutum shi kaɗai da zamantakewa.
Madogara: Tarihin Imam Ali (a.s), Al-Murtaza Al-Amil
Your Comment